Fadar white house a Washington ta bada sanarwan takatar da wani muhimmin taro tsakanin Amurka da HKI dangane da JMI, ta wanda aka shira gudanar da shi a gobe Alhamis.
Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto kamfanin dillancin labaran Axios yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa fadar white house ta dauki wannan matakin ne don maida martani ga firai ministan HKI Benyamin Natanyahu, wanda ya watsa wani faifain bidiyo inda a ciki yake zargin gwamnatin shugaban Biden da dakatar da turawa HKI wasu kunshin makamai har guda biyu.
Wani jami’in fadar whiye house ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Axios kan cewa bidiyon Natanyaho ya bata al-amura da dama, ya kuma kara da cewa jami’an gwamnatin HKI suna kan hanyarsu ta zuwa washinton don halattan wannan taron mai muhimmanci kan JMI.
Wani jami’in ya bayyana cewa an dage lokacin taron ne amma ba’a dakatar da shi gaba daya ba, s
Wani jami’in gwamnatin Amurka Hochstein, wanda ya yada zango a Telabib bayan ya je kasar Lebanon don kokarin ganin an dakatar da bude wuta kan arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye ya fadawa Natanyahu, maganganunsa a bidiyon bai dace ba kuma bai kamata yayi su a yanzun ba.