El-Barade’i Ya Bayyana Cewa; Barazanar Trump Na Kai Hari Kan Iran Karya Dokokin Kasa Da Kasa Ce

Tsohon shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya El-Baradei ya bayyana cewa: Barazanar Trump na kai hari kan Iran a fili take karya dokokin duniya ce

Tsohon shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya El-Baradei ya bayyana cewa: Barazanar Trump na kai hari kan Iran a fili take karya dokokin duniya ce

Tsohon Darakta Janar na Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya kuma tsohon Mataimakin Shugaban Masar Muhammad El-Barade’i ya yi gargaɗi game da barazanar da Amurka ke yi na kai hari kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, yana mai ɗaukar barazanar a matsayin keta dokokin ƙasa da ƙasa kuma yana tunasar da yanayin da ya gabaci yaƙin Amurka da Iraki.

A cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na X, El-Baradei ya bayyana cewa: Barazanar da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi na kai hari kan Iran, ba tare da wata hujjar bullar barazana a fili ba, ta zama keta dokokin ƙasa da ƙasa. Ya lura da cewa: Waɗannan barazanar suna tunatar da shi yaƙin da ba bisa ƙa’ida ba da rashin da’a kan Iraki, musamman ƙaryar da ke tare da ita, da kuma mummunan sakamakon da ya biyo baya.

El-Barade’i ya ƙara da cewa: “Rusa rayuwar ɗan adam ko lalata yankinsu – fiye da halin da ake ciki – ba su da wani amfani… ” yana mai nuni da ci gaba da manufofin da ke barazana ga tsaro da kwanciyar hankali na yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted