Ba wannan ne karon farko wanda mutanen Najeriya suka fuskantar duhu a duk fadin kasar saboda lalacewar tsarin bada wutan lantarki da samar da shi ba.
Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa a jiya litinin babu wutan lantarki a duk fadin kasar saboda lalacewar tsarin samarwa da kuma rarrabawa wutan lantarki a kasar.
Labarin ya kara da cewa an dauke wutan lantarki a duk fadin kasar ne da misalign karfe 7 na yamma, kuma daukarwar ya game dukkan kasar. Ya ce dukkan injuna samar da wutan lantarki guda 22 da ake da su a kasar sun mutu a lokaci guda.
Kuma tun lokacin ya zuwa yanzu da ake bada wannan labarin hukuma mai kula da wutan lantarki a kasar bata fadi kome dangane dauke wutar ba.