Dubban yahudawan sahayoniyya ne suka gudanar da zanga-zangar neman kulla yarjejeniyar sakin ‘yan uwansu da suke hannun ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa
Rahotonni sun bayyana cewa: Dubban yahudawan sahayoniya sun gudanar da zanga-zanga a jiya Asabar a yankuna daban-daban na Falasdinu da aka mamaye domin neman gwamnatinsu ta kulla yarjejeniyar musayar fursunoni da bangaren ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa don hanzarta sakin yahudawan da aka kama a matsayin fursunonin yaki da kuma hanzarta gudanar da zabe don kawo karshen gwamnatin fira ministan haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu.
Jaridar haramtacciyar kasar Isra’ila ta Yedioth Ahronoth ta ce: Dubban yahudawa sahayoniyya ne suke halartar zanga-zangar da ake shiryawa a duk mako a dandalin Kaplan da ke tsakiyar birnin Tel Aviv, inda suke rera taken bukatar cimma yarjejeniyar musayar fursunoni cikin gaggawa da za ta kai ga sakin fursunonin yahudawan sahayoniyya da ake tsare da su a Gaza, kuma a halin yanzu zanga-zangar ta fadada a cikin yankunan da aka mamaye zuwa kusan yankuna 50.