Trump Yana Goyon bayan Shawarar Putin Kan Musayar Kasa Don Zaman Lafiya Da Ukraine

 Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fadawa shuwagabannin kasashen turai kan cewa ya amince da shawara shugaba Putin na musayar kasa don samar da zaman

 Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fadawa shuwagabannin kasashen turai kan cewa ya amince da shawara shugaba Putin na musayar kasa don samar da zaman lafiya.

Majiyoyi biyu wadanda basa son a bayyana sunayensu kuma kusa da Trump a taron na Alaska ya bayyanawa jaridar ‘The guardian’ ta kasar Burtania a jiya Asabar kan cewa, Trump ya fadawa masu kan cewa Zeleski ya amince da mikawa Putin Dombasa sannan rasha kuma zata tsaya inda take, ba zata karbi sauran yankunan Donbas da suke hannun Ukraine ba.

Don haka putin ya dage kan cewa dole Ukraine ta fice daga Dobas Kwata-kwata. Labarin ya ce har yanzun Ukraine tana iko da Kramatorsk da Sloviansk a yankin Donestk.

Sannan yankunan kudancin Ukraine Kherson da Zaporizhzhia, inda sojojin Rasha suke rike da su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted