Wasu gungun dalibai daga jami’ar Stanford ta Amurka dauke da tutocin Falasdinu, sun bayyana goyon bayansu ga al’ummar Gaza da ake zalunta.
Jaridar LA Times ta kasar Amurka ta bayyana cewa, bayan gagarumin gangamin da aka yi a jami’ar Stanford don nuna goyon baya ga al’ummar Gaza, ana ci gaba da gudanar da zanga-zangar nuna adawa da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Falasdinu a wannan jami’a.
Hotunan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta sun nuna daruruwan dalibai sun yafa tutocin falastinu a kawunansu, yayin da kuma wasu suke rike da tutocin a hannunsu.
Wata kungiyar dalibai masu goyon bayan Falasdinu ce ta shirya gangamin wanda ya karfafa gwiwar dalibai da su nuan jajircewa wajen nuan matsayarsu kan kin ayyukan kisan kiyashi da Isra’ila take aikatawa kan fararen hula a Gaza.
Kakakin kungiyar ya gabatar da jawabi a gaban gangamin, inda yake cewa: Kun kafa tarihi da zama da ba a taba ganin irinsa ba,
A bana dai Stanford ta kasance wurin da dalibai suke nuna matsayinsu na ‘yan adamtaka, tare da nuna rashin amincewa da kisan kare dangi da ake yi wa mata da kananan yara a Gaza, wannan babban lamari a tarihin wannan jami’a da dalibanta masu jajircewa.
A cikin ‘yan watannin da suka gabata, masu zanga-zangar sun kafa wani babban sansani a harabar jami’ar wanda ya zama mafi dadewa zama a tarihin Stanford.
Ana zargin Isra’ila da aikata kisan kiyashi a kotun kasa da kasa. A wani hukunci da kotun ta yanke, ta umurci gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da ta gaggauta dakatar da ayyukanta a Rafah, inda Falasdinawa sama da miliyan guda suka fake.