Daliban jami’ar ‘Queen Mary’ dake gabacin birnin London na kasar Butania sun shiga sahun daliban jami’o’ii a kasar Burtaniya wadanda suke goyon bayan Falasdinawa a Gaza, suke kuma yinn allawadai da gwamnatocin kasashensu masu tallafawa HKI a kisan kiyashin da sukewa al-ummar Falasdinu wacce aka mamaye kasarsu kimani shekaru 76 da suka gabata.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa daliban jami’ar ta Queen Mary’ sun bayyana goyon bayansu ga falasdinawa masu gwagwarmaya da sojojin HKI don dawo da kasarsu da aka kwace, sun kuma bukaci hukumomin jami’ar su yanke dukkan alaka ko dangantaka da HKI da kuma kamfanonin makamai wadanda suke da hannu a zubar da jinin Falasdinawa a Gaza.
Tun ranar 17 ga watan Afrilun day a gabata ne daliban jami’ar Colombia na birnin New Yorka suka fara borewa gwamnatin kasar tare da bukatar a kawo karshen yaki a gaza a kuma dakatar da kissan kare dangi da ke faruwa a Gaza. Daruruwan daliban jami’o’ii a kasashen Amurka Burtania, Faransa, Jamus da wasu kasashen Turai ne suka bi sahun wadandan nan daliban tare da wannan manufa.
Gwamnatocin Amurka Burtania, Jamus, Faransa da sauransu sun yi kokarin hana boren daliban yaduwa zuwa sauran jami’o’ii, tare da amfani da karfi amma ya zuwa yanzu sun kasa yin hakan.
Development ProgramTehran, I.R. Iran
Mobile: +98-912-8102861