Iran: IRGC Sun Ce Batun Samar Da Sabon Yankin Gabas Ta Tsakiya Mafarki Ne

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun bayyana cewa: Batun samar da sabuwar yankin Gabas ta Tsakiya a ƙarƙashin ikon ‘yan sahayoniyya “rudun

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun bayyana cewa: Batun samar da sabuwar yankin Gabas ta Tsakiya a ƙarƙashin ikon ‘yan sahayoniyya “rudun tunani ne kawai”

A cikin wata sanarwa da dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran suka fitar, sun yi kakkausar suka ga yadda Amurka da ‘yan sahayoniyya suke amfani da halin da ake ciki na rashin zaman lafiya a kasar Siriya da wuce gona da iri kan kasar da kuma mamaye yankunan kasar da suke yi gami da kai hare-hare kan ababen more rayuwa da muhimman cibiyoyi na wannan kasa, Iran din tana jaddada wajabcin kiyaye ‘yancin kan kasar Siriya, mutunta kasar a matsayar ‘yantacciyar kasar.

Hari ila yau, Dakarun kare juyin juya halin Musuluncin sun yi Allah wadai da kakkausar murya kan yadda Amurka da ‘yan sahayoniyya suke cin gajiyar halin rashin zaman lafiya a kasar Siriya a halin yanzu, tare da daukar hare-haren wuce gona da irin ‘yan sahayoniyya kan ababen more rayuwa da muhimman cibiyoyin wannan kasa a matsayin cin zarafi.

Sanarwar ta kuma jaddada muhimmancin kiyaye ‘yancin kan kasar Siriya da hadin kan kasar, tare da yin la’akari da cewa abubuwan da suka faru a baya-bayan nan darasi ne masu fa’ida da ke kara habaka ci gaban gwagwarmaya da kara azamar korar Amurka daga yankin da kuma cimma manufofin al’ummar musulmi ta hanyar ‘yantar da Qudus mai alfarma da kuma kawar da cutar daji da yahudawan sahayoniyya ke wakilta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments