Shugaban kasar Cuba miguiel Diaz –canel yayi tir da matakin da kwamitin dake bada kyautar noble a duk shekara ya dauka na bada kyatutar ta wannan shekarar ta 2025 ga yan adawar kasar venuzela maria corina machado inda ya bayyana shi a matsayin abin ban kunya .
Matakin na Diaz canel yana nuna irin yanayin zaman tankiya tsakanin gwamnatocin latin Amurka da kuma kasashen yamma , kuma yana nuna cewa rabuwar kawuna kan wanda aka amince shi a matsyin mai inganci a bangaren dimokuradiya kuma ya haifar da rashin zaman lafiya a yankin.
Yana mai cewa babban abin kunya ne ace kyutar Nobel ta zaman lafiya a mika ta ga wadda ta janyo tsoma bakin sojoji a kasarta,
Wannan yana nuna irin rarrabuwar kayi da aka samu a fadin latin Amurka game da maa’nar zaman lafiya da demokuradiya.