China Da Rasha Sun Gudanar Da Atisayen Hadin Giwa Bayan Barazanar Kungiyar Tsaro Ta Nato

Kasashen Chaina da Rasha sun fara atisayen soje na hadin giwa bayan barazanar kungiyar tsaro ta Nato karkashin jagorancin Amurka. Tashar talabijin ta Presstv a

Kasashen Chaina da Rasha sun fara atisayen soje na hadin giwa bayan barazanar kungiyar tsaro ta Nato karkashin jagorancin Amurka.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa an sayawa atisayen suna ‘Hadin giwa teku na 2024’ kuma an fara atisayen a garin Zhanjiang na lardin Guangdong a jiya Lahadi. Sannan wannan atisayen zai ci gaba har zuwa tsakiyar watan yulin da tsakiyar yuli.

Tashar talabijin ta CCTV ya bayyana ma’aikatar tsaron kasar Chaina na cewa a halin yanzu sojojin kasar Rasha suna iko da arewa maso yammacin tekun pecific, sannan wannan atisayen bai da nufin takalar wata kasa.

Labarin ya kara da cewa a cikin wannan atisayen za’a gwada makamai masu linzami kuma garkuwa ga makamai. Har’ila yau zasu gwada dabarbarun kare kai daga makamai dabam daban.

A ranar labaran da ta gabata ce a taron kasashen kungiyar tsaro ta NATO 32 a birnin Washington suka bayyana China a matsayin kasa wacce take taimakawa Rasha a yakin da suke fafatawa da ita a Ukraine. Kuma sun ware dalar Amurka biliyon 43 don taimakawa kasar ta Ukraine.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments