Limaman masallatai har 400 a kasar Burtaniya sun yi tir da abinda gwamnatin kasar ta bayyana shi ne ma’anar ta’addanci a wajenta, kuma da wannan ma’anar zata sanya ido a kan wasu kungiyoyin musulumi a kasar wadanda ta amabata.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wani bayani wanda limaman suka fitara a yau Asabar kan cewa wannan sabon ma’anar da sakataren harkokin cikin gida Michael Gove ya bayyana wani shiri ne na cutar da al-ummar musulmi a kasar.
Labarin ya kara da cewa a cikin wani jawabinda da sakataren yayi a makon da ya gabata ya nuna yastar hannu kan kungiyar musulmi ta
‘Muslim Association of Britain (MAB) da kungiyar CAGE ta musulmi da wasu kungiyoyin a matsayin wadanda sabuwar dokar ta’addanci zata sanya ido a kan yayansu, ta kuma dauki matakan da suka dace a kansu saboda kin da suke nunawa yahudawa.
Bayanin ya kara da cewa a baya a san Michael Gove da goyon bayan HKI da kuma yahudawa a kasar kuma ya sha sukan musulmi da addinin musulunci a fili.
Bayanin ya kammala da cewa wannan sabuwar dokar tana son kara karafa makiyan musulmi a kasar ta Burtania da kuma bata zamantakewa mai kyau dake tsakanin mutane mabiya addinai daban daban a kasar.