Wani bincike mai zaman kansa da masana daga jami’ar London a sashen (LSHTM), suka gudanar ya nuna cewa adadin mutanen da suka mutu a hare-haren Isra’ila da Gaza ya zarce wanda ake gayi.
Ana rage adadin mutunen da suka mutu a hare-haren Isra’ila a Gaza da kimanin kaso 41 inji bincikne inda aka kashe kashi uku cikin dari na jama’ar yankin a yakin da ake yi.
Binciken ya kiyasta cewa mutanen da suka mutu saboda hare-haren a Gaza sun kai 64,260 daga 7 ga Oktoban 2023 zuwa 30 ga Yulin 2024, idan aka kwatanta da 37,877 da Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta ba da rahoto.
Sakamakon binciken, wanda aka wallafa a mujallar lafiya ta The Lancet a ranar Juma’a, ya nuna cewa akalla kashi uku na mutanen Gaza sun mutu sakamakon yakin, inda wasu alkaluman suka nuna cewa kaso 59 daga cikinsu mata ne da yara da tsofaffi.
Binciken ya gano cewa, yawan mutanen da suka mutu zuwa Oktoban 2024 ya haura 70,000, wanda a lokacin ma’aikatar lafiya ta ce kimanin 42,000 aka kashe.
Wadanda suka jagoranci wallafa binciken sun bukaci daukar matakin gaggawa wajen shiga tsakani don kare fararen hula da dakatar da yakin.