Bayanin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Dangane Da Kai Wa HKI Hari

A wani bayani da ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar musulunci ta Iran ta fitar ta bayyana cewa; A karkashin dokar MDD mai lamba 51 Sojojin Iran

A wani bayani da ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar musulunci ta Iran ta fitar ta bayyana cewa; A karkashin dokar MDD mai lamba 51 Sojojin Iran sun mayar da martani akan wuce gona da iri na ‘yan sahayoniya wanda ya yi sanadiyyar shahadar masu bayar da shawarar soja ga gwamnatin Syria.

Bayanin na ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar musulunci ta Iran ya kuma ce; Iran ta yi azamar kare kasarta da manufofinta a gaban duk wasu masu wuce gona da iri.

Wani sashe na bayanin ya kuma ce; Jamhuriyar musulunci ta Iran ba za ta yi taraddudin sake daukar wani mataki irin wannan ba domin kare manufofinta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments