Bankin Raya Afirka ( AFDB) Ya Bayyana Kasashen Da Tattalin Arzikinsu Yake Bunkasa Da Sauri A Cikin Nahiyar

Bankin Raya Afirka ya sanar da wasu kasashe 10 da ya ce, su ne tattalin arzikinsu yake bunkasa da sauri a cikin nahiyar, tare da

Bankin Raya Afirka ya sanar da wasu kasashe 10 da ya ce, su ne tattalin arzikinsu yake bunkasa da sauri a cikin nahiyar, tare da yin hashashen cewa  gabashin Afirka zai zama  sama da sauran  yankunan nahiyar a cigaba.

Ana hasashen cewa  a cikin  rabin kasashen nahiyar za a sami habakar jumillar kudaden shiga ( GDP)  daga 4.4% da ya kasance a 2024, ya koma 6.1% a cikin 2026. Sai kuma a cikin kasashen  Rwanda, Uganda, Sudan Ta kudu, Habasha, Tanzania da Kenya mafi karancin karuwarsa zai zama  kaso 5.% a 2025.

A cikin yankin yammacin Afirka kuwa, an tsinkayo cewa tattalin arzikinsu zai tashi daga 4.1% a 2024,zuwa 4.6% a 2025, kuma kasashe irin su Togo, Benin, Cote De Voire, da Gambiya za su sami bunkasa mai karfi.

A Arewacin Afirka kuwa jumillar kudaden shiga ( GDP) zai tashi daga 2.7% a 2024, zuwa 4.2 a 2026.

Kasar Sudan  Ta Kudu ce ake hashshen cewa za ta zama zakara a fadin nahiyar ta Afirka wajen bunkasar jumillar kudaden shiga da kaso 34.4%,saboda sake dawowar hako man fetur da kuma fitar da shi zuwa kasuwannin duniya.

Ita kuma Senegal tattalin arzikin nata zai bunkasa ne da kaso 8.9% saboda man fetur, iskar Gas, muhimman cibiyoyi da kuma noma da kiwo.

Kasashen jamhuriyar Nijar, Djibouti, Togo Habasha da Benin da Coye De Voire za su samun bunkasa da kaso 6.3.6.9.% saboda zuba hannun jari a cibiyoyi masu muhimmani da gina su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments