Sashen ‘Sahab’ na hukumar gidajen radiyo da talabijin na kasar Iran ya cika shekara guda da fara aiki.
A lokacin bukukuwan da aka gudanar a jiya Asabar, shugaban hukumar gidajen radiyo da talabijin na kasar Peyman Jebeli ya yabawa shugaban bangaren Sahaba, da kuma ma’aikatansa. Kan irin kokarin da suka yi a cikin shekara guda da ta gabata.
Tashar talabijan ta Presstv mai watsa shiryensa da harshen turanci ya nakalto Jebilli ya na cewa,za’a bude tashar Presstv ta harshen turkanci da kuma sashem Hispa TV da harshen Purtigal.
A bangarensa shugaban Sahaba kuma, wato Hossein Sheikhian ya ce an kafa sashen na sa ne a ranar 21 ga watan Jenerun shekara ta 2023. Kuma manufar kafa shi ne wayar da kan mutane da kuma isar da sakon JMI ga masu sauraro da kallo daga kasashen waje.
Sashen Sahab dai yana da tashoshin radiyo da talabijin, masu yawa, wadanda wasunsu, suna aiki tun kafin jiyun juya halin musulunci a kasar. Amma mafi yawan tashoshin radiyo da talabijan karkashin sahab an budesu bayan nasara juyin juya halin musulunci a kasar.
Sashen Rasha ya fara aiki tun shekara ta 1946, Uzbek 1992. Sai kuma radiyo Dari 1980, da kuma Radio Taleshi 2004.
Sauran sun hada da Jamusanci, Espaniyanci, Albanianci, Ingilishi, Italianci, Faransaci, Swahili, Hausa, Bengali, Japananci, Chinanci, Malaya, Hindu, turkancin Istanbul, Armenianci, Kazakhanci, Azerianci, Assyrianci, Tajikanci, Turkmenci, larabci, Hebranci, da kuma Pashtonci ne aka bude su a cikin wannan lokacin.. Har’ila yau duk tashohsin suna da shafuka na intanet da wasu kafafen sadarwa na yanar gizo duk karkashin Sashen Sahab.