Bagher Qalibaf, Ya Sake Zama Kakakin Majalisar Dokokin Iran

Majalisar dokokin Iran ta sake zaben Mohammad Bagher Qalibaf a matsayin kakakin majalisar na tsawon shekara guda. An zabe shi da kuri’u 197 daga cikin

Majalisar dokokin Iran ta sake zaben Mohammad Bagher Qalibaf a matsayin kakakin majalisar na tsawon shekara guda.

An zabe shi da kuri’u 197 daga cikin 287.

Zaben dai ya zo ne kwana guda bayan taron kaddamar da majalisar da kuma rantsar da sabbin mambobin majalisar su 290 da aka zaba.

Maido da Qalibaf kan mukaminsa na zuwa ne gabanin zaben shugaban kasar Iran a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zaben fidda gwani na zaben da za’a gudanar a ranar 28 ga watan Yuni bayan shahadar shugaba Ebrahim Raeisi a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu.

A ranar Litinin ne sabuwar majalisar ta fara wa’adinta na shekaru hudu.

A cikin sakon da ya aike wa majlaisar,Jagoran Juyin Juya Halin Muuslinci na kasar, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya kira majalisar dokokin kasar da nuna ci gaban dimokuradiyyar addini a Iran, ya kuma shaida wa ‘yan majalisar da su kiyaye muradun kasa.

An gudanar da zaben ‘yan majalisar dokokin Iran a watan Maris, inda ‘Yan takara 245 ne suka lashe zaben a zagayen farko.

Daga bisani an gudanar da zaben cike gibi na ‘yan majalisar a ranar 10 ga watan Mayu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments