Larijani: Iran Zata Mayar Da Martani Mai Tsanani Kan Duk Wanda Ya Kai Mata Hari

Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya jaddada cewa: Iran za ta mayar da martani da karfi kan duk wani wuce gona da

Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya jaddada cewa: Iran za ta mayar da martani da karfi kan duk wani wuce gona da iri kanta

Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya bayyana cewa: Gwagwarmaya ita ce babban jari kuma wata dabara mai kima ga yankin, yana mai jaddada cewa: Iran za ta mayar da martani mai karfi kan duk wani hari da aka kai mata, kuma babu wata tattaunawa da za ta yi tasiri a karkashin tunanin Amurka na “zaman lafiya da nuna karfi.”

Ali Larijani ya jaddada a shirye Iran take a koda yaushe ta mayar da martani mai karfi kan duk wani hari da gwamnatin mamayar Isra’ila za ta kai kan kasar Iran, yana mai cewa “Haramtacciyar kasar Isra’ila ba za ta bar yankin Gabas ta Tsakiya ya zauna lafiya ba, muddin Netanyahu na kan karagar mulki, ba zai bari al’amura su daidaita ba, ko da a Falastinu.”

Yana mai jaddada cewa; Netanyahu mugun mutum ne mai haifar da rikici don amfanin kansa.

A wata hira ta musamman da ya yi da tashar talabijin ta Al-Mayadeen, Larijani ya kara da cewa: “Benjamin Netanyahu mugun mutum ne kuma ba zai bari al’amura su daidaita ba, a kullum yana kai hari kan kasar Lebanon da ma wasu kasashe, domin daga hakula a kasashen, kuma an ga abin da ya yi a kasar Siriya, wannan hargitsin tsaro da yake haddasawa a kasashe abu ne da ba za a amince da shi ba.”

Hukumar yada labaran Isra’ila ta watsa rahoton cewa, tun farkon yakin Gaza, kimanin sojoji 3,770 ne aka tabbatar sun kamu da rashin lafiya kwakwalwa saboda da tashe-tashen hankula.

Share

5 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments