Majalisar Dinkin Duniya ta jaddada cewa: Halin da ake ciki a Gaza yana kara muni da zama bala’i
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya bayyana halin da ake ciki a Zirin Gaza a matsayin “mai ban tsoro da bala’i”, yana mai gargadin cewa yanayin da Falasdinawa ke fuskanta a yankin na iya zama “manyan laifuffukan yaki na kasa da kasa.”
A cikin jawabin da mataimakiyarsa Amina Mohammed ta karanta a yayin taron “Karfafa ayyukan jin kai a Zirin Gaza”, wanda aka gudanar a birnin Alkahira na kasar Masar a jiya litinin, Guterres ya bukaci al’ummun kasa da kasa da su gina tubalin wanzar da zaman lafiya mai ɗorewa a Gaza da kuma a duk faɗin Gabas ta Tsakiya.
Babban sakataren na Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada cewa: Rashin abinci mai gina jiki ya bazu a Gaza ga masifar yunwa da ta tunkaro. Sannan a halin da ake ciki, tsarin kiwon lafiya ya ruguje.