Babban Sakataren Kungiyar Hizbullah Ya Jaddada Cewa Kungiyarsa A Shirye Take Ta Ci Gaba Da Yaki

Babban sakataren kungiyar Hizbullahi ya jaddada cewa: Ba ​​su son yaki, amma suna son ci gaba goyon bayan Gaza kuma a shirye suke su ciga

Babban sakataren kungiyar Hizbullahi ya jaddada cewa: Ba ​​su son yaki, amma suna son ci gaba goyon bayan Gaza kuma a shirye suke su ciga ba da yin yaki

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Qassim ya jaddada cewa: Ba su son yaki, amma suna son ci gaba da goyon bayan Gaza, kuma a shirye suke su ci gaba da yin yaki idan aka tilasta musu kare kai da goyon bayan al’ummar Gaza.

Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Qassim ya sanar da cewa: Hare-haren wuce gona da irin haramtacciyar kasar Isra’ila na da matukar hadari da kuma raɗaɗi, amma duk da haka, kungiyar Hizbullahi ta zage dantse da himmatuwa tare da samun nasarar shawo kan matsaloli da kare kasa.

Babban sakataren kungiyar ta Hizbullah ya kuma jaddada cewa: Tsayin dakan ‘yan gwagwarmaya na al’ada ya tsorata makiya, kuma hasarar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi na da yawa, kuma Hizbullahi ta samu babbar nasara da ta zarce nasarar da ta samu a shekara ta 2006.

Sheikh Na’im Qassim ya ce: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta na sa ran cimma burinta cikin dan gajeren lokaci bayan ta dakile tsarin shugabanci da wani bangaren karfin da kungiyar ke da shi.

Ya kara da cewa: Kungiyar Hizbullah ta iya tsayawa tsayin daka a fagen daga inda ta fara kai hare-hare kan cikin gidan makiya, lamarin da ya sanya aka samu muhimmin yanayi na tsaro.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments