Babban kwamandan dakarun IRGC na kasar Iran Burgediya Janar Hussain Salami ya bayyana cewa a dai dai lokacinda manya-manyan kasashen duniya suke amfani da takunkuman tattalin arziki, mafi muni a kan wasu kasashe, a lokacin ne kuma, dakarun IRGC suke yunkuri don kare kammu daga makiya. Sannan samar da ci gaban da muke bukata don kawukammiu daga cikin gida.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Salami yana fadar haka a jiya Alhamis, ya kuma kara da cewa, JMI ta na samun ci gaba duk tare da matsin lambar da ta take ciki. Kuma zata kara karfin sojojinta, don kare kanta daga duk wata kasa wacce teka barazana ga cibiyoyon Nukliyar kasar ko kuma tana son ta maida kasar mu baya.