Babban Hafsa Hafsoshin Sojin Iran: Makiya Sun San Babban Matsalar Duk Wani Hari Kan Iran

Babban hafsan hafsojin sojin Iran ya bayyana cewa; Makiya sun san illar duk wata kasada ta soja Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Iran, Manjo Janar Seyyed

Babban hafsan hafsojin sojin Iran ya bayyana cewa; Makiya sun san illar duk wata kasada ta soja

Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Iran, Manjo Janar Seyyed Abdulrahim Mousavi, ya tabbatar da cewa: Makiya Iran sun san illar duk wata kasada ta soja da za a yi da Iran, yana mai gargadin cewa duk wani hari da za a kai za a mayar da martani mai tsauri.

Manjo Janar Mousavi ya fitar da wannan sanarwa ce a ranar Sojojin Sama na Iran, inda ya jaddada cewa, duk wani matakin soja da za a dauka kan Iran zai haifar da hasarar da ba za a iya jurewa ba ga makiya, wanda a karshe zai kai ga shan kaye a dabarunsu da kuma kara ta’azzara rikicin zuwa wani mataki na yanki.

Mousavi ya nuna cewa: Sojojin Iran suna cikin shiri da cikakken hadin kai, a shirye suke su mayar da martani mai kaushi ga duk wata barazana. Ya jaddada cewa martanin da za a mayar ga duk wani hari ko kuskuren lissafi daga abokan gaba zai kasance cikin sauri da kuma zafi.

Ya kara da cewa sojojin na ci gaba da karfafa karfinsu na soja da kuma inganta shirye-shiryensu na kariya daidai da karuwar barazanar, a cikin tsarin kiyaye kariya da kuma kare tsaron kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted