Babban Bankin Nijeriya CBN, ya sake bayar da wani dauki a Kasuwar hada-hadar musayar kudade, da nufin samar da sauki wajen samun kudade a cikin kasar.
Hakan ya sanya Bankin, ya sayar da dala miliyan hamsin, ga dilolin da aka yarjewa yin hada-hadar musayar kudade a cikin kasar.
Kazalika, Bankin ya yi hakan ne, domin samar da daidaito, wajen yin hada-hadar musayar kudaden
Naira dai, ta fara fuskantar tarnaki ne, biyo bayan samun raguwarta a kasuwar hada-hadar musayar kudade, inda kuma bukatar dalar, ya kara karuwa.
Tun bayan da Naira ta samu farfadowa, Bankin na CBN, ya samu sauki kan hada-hadar musayar kudaden da aka yi.
Sai dai, Bankin na CBN ya tura dala miliyan hamsin musamman domin dillalen da aka yarjewa, su samu kudaden da yin hada-hadar da dama.