Ayatullahi Siddiqi Ya Ce: Amurka Ba Ta Mutunta Duk Wata Yarjejeniya Ballantana Alkawari

Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran ya bayyana cewa: Iran ba ta taba samun girmamawa daga tattaunawar da tayi da Amurka ba

Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran ya bayyana cewa: Iran ba ta taba samun girmamawa daga tattaunawar da tayi da Amurka ba

Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran a yau, Ayatullahi Kazim Sadiqi ya bayyana cewa: Iran ba ta taba samun girmamawa a zaman tattaunawan da ta yi da Amurka a baya ba, kuma babu wani ci gaba da zaman tataunawan ya taba kawo wa kasar ta Iran. Saboda Amurkawa ba sa daukan kansu a matsayin wadanda ya dace su yi biyayya ga dokokin ƙasa da ƙasa ko mutunta duk wata yarjejeniyar da aka cimma da su.

Ayatullahi Siddiqi ya jaddada cewa: Tsoron Allah shi ne mafi kyawun siffa ga dan Adam, don haka ya jaddada yin kira ga al’umma su kasance masu tsoron Allah a dukkan harkokinsu na rayuwa, yana mai fayyace cewa: Idan a kullum mutum yana kiyaye tsoron Allah a fagen rayuwarsa misalin maganganunsa, dabi’unsa, alakarsa da iyalansa, makwabtansa, da kiyaye dokokin Allah ta hanyar kauracewa abububwan da ya haramta, da kokarin aikata abubuwan da ya halarta, to babu shakka Allah zai dauki matakin Sanya albarka a fagen rayuwarsa tare da Sanya mutum ya yi kyakkyawan karshe.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments