Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yaba da kokarin gwamnati da al’ummar Iraki wajen karbar bakwancin masu ziyarar juyayin Arba’een na Imam Husaini {a.s}.
A yayin da yake halartar shirin na musamman na “muryar ku a ko’ina” da ake watsawa a gidan rediyon Saba, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya tattauna batutuwan da suka shafi gagarumin tattakin Arbaeen da tasirinsa ga duniyar musulmi.
A farkon hirar, minista Araqchi ya mika sakon gaisuwarsa ga masu ziyarar Arba’een a birnin Karbala, inda ya bayyana farin cikinsa da halartar wannan gagarumin taron juyayi. Yana mai jaddada cewa: “Wannan tattakin babbar yunkuri ne na ‘yan Shi’a, kuma tasirinsa na kasa da kasa yana da matukar muhimmanci, babu wani taro mai girman wannan a duk fadin duniya a duk tsawon shekara.”