Araqchi: Iran za ta ci gaba da bayar da cikakken goyon baya ga Syria wajen tinkarar Isra’ila

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Tehran za ta ci gaba da bayar da cikakken goyon baya ga kasar Siriya da kuma fafutukar

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Tehran za ta ci gaba da bayar da cikakken goyon baya ga kasar Siriya da kuma fafutukar tsayin daka don tinkarar mamayar da Isra’ila ke yi a yankin.

Araghchi ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad a birnin Damascus a wannan Asabar a kasar Siriya zango na biyu na rangadin da yake yi a yankin bayan muhimmiyar ziyararsa  a kasar Lebanon.

“Wannan matakin na Iran ya yi daidai da kare zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin da kuma tallafawa tsaron kasashen yankin,” in ji shi.

A nasa bangaren shugaban kasar Siriya ya yaba da irin matsayar Iran na goyon bayan al’ummar Palastinu da ake zalunta da kuma ‘yancin kare kai da kuma gwagwarmayarsu wajen  tinkrarar ayyukan mamaya da wuce gona da iri na Haramtacciyar Kasar Isra’ila.

Assad ya ce dole ne kasashen duniya su yi kokarin kawo karshen bala’in da Isra’ila ke haifarwa a yankin.

Kamfanin dillancin labaran SANA na kasar Siriya ya nakalto shugaban kasar Siriya yana cewa; gwagwarmaya da duk wani nau’i na mamaya da wuce gona da iri da kuma kisan jama’a hakki ne halastacce na kowace al’umma.

Ya yaba da martanin  da Iran ta mayar game da hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kaiwa kan kasashen yankin da keta huruminsu.

Ya kuma kara da cewa martanin da sojojin Iran suka mayar  a daren Talata ya ba da bababn darasi ga sahyoniyawa.

n cewa turbar juriya tana da karfin dakile makiya da kuma

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments