Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Akaci ya bayyana cewa; Idan har kasar Birtaniya tana ci gaba a kiran Iran ta dakatar da tace sanadarin uranium a cikin kasarta, to kuwa Iran din za ta yanke tattaunawar da take yi da ita.
Ministan harkokin wajen na jamhuriyar musulunci ta Iran ya rubuta a shaifnsa na hanyar sadarwa ta jama’a cewa: Iran ta tuntubi Birtaniya ne da kyakkyawar manufa,haka nan sauran kasashen turai da aka yi yarjejeniyar Nukiliya da su, duk da cewa, Amurka ba ta son su shiga cikin tattaunawar.”
Arakci ya kuma ce; Idan har matsayar Birtaniya shi ne ta ga an daina tace sanadarin uranium baki daya a cikin Iran, wanda hakan keta yarjejeniyar da ita kanta tana ciki ne, a yanayi irin wannan za a daina Magana da ita akan abinda ya shafi Shirin Iran na makamashin Nukiliya.” Arakci yana mayar da martani ne akan maganar da jakadan Birtaniya a Washington Peter Mandelson ya yin a cewa; kasarsa tana goyon bayan Shirin Shugaban kasar Amurka Donald Trump na kawo karshen Shirin Iran na makamashin Nukiliya.