Aragchi: Shirin Nukliyar Kasar Iran Na Tafiya Kan Fahintar Rashin Amincewa Da Babakere

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa JMI ta gina shirinta na makamashin nukliya ne kan fahinta da kuma kundin tsarin mulkin

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa JMI ta gina shirinta na makamashin nukliya ne kan fahinta da kuma kundin tsarin mulkin kasar wanda yayi tir da mamaya da kuma babakere.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a safiyar yau Asabar a hubbaren Imam Ruhullah Al-khomaini (q) wanda ya kafa JMI. Ministan da sauran manya-manyan ma’aikata a ma’aikatar harkokin wajen kasar sun je hubbaren Imam ne don jadda bai’a ko alkawali da shi kan tafiya a kan tafarkin da ya barsu a kai.

A cikin wani wuri a Jawabinsa Ministan ya kara da cewa a cikin kundin tsarin mulkin JMI ya zo kan cewa Iran ba zata danne wata kasa ba kuma ba zata amince da danniyaba, hakama ba zata zalunci wata kasa ba kuma ba zata yarda a zalunceta ba.

Ya ce abinda gwamnatin kasar Amurka take son tayiwa JMI shi ne danniya da zalunci, Kalmar kada ku ce makamacin Uranium kanta danniya ce. Su sun amincewa kansu su mallaki makaman nukliya amma ba zasu amincewa wata kasa ta ma tashe makamashin uranium wanda yarjeniyar NPT ta amince masu su tace ba. Don haka wannan baa bin amincewa ne ga JMI ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments