Aragchi: Mutane Masu Wayo Maimakon Takurawa Ta Koli Su kan Zabi Hankali Mafi Koli

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi, a lokacin da yake maida martani ga jawabin shugaban kasar Amurka Donal Trump a jiya Laraba, ya ce

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi, a lokacin da yake maida martani ga jawabin shugaban kasar Amurka Donal Trump a jiya Laraba, ya ce takurawa mai tsanani ya karya.

Abbas Aragchi ya fadi haka a jiya Laraba , ya kuma kara da  cewa bayan takuarawa masu tsanani Amurka tana bukatar tattaunawa da Iran. Harma ya zauna da shugaban kasarta.

A wani bangare na maida martanin Aragchi ya bayyana cewa dangane da fadinsa, ba zai taba amincewa Iran ta mallaki makaman Nukliya ba, yace Iran mamba ce a yarjeniyar NTP, a kuma hukumar makamashin nukliya ta IAEA. Zasu lamunce masa kan cewa Iran bata bukatar makaman nukliya.

Amma duk da haka Iran ba zata taba sayar da hakkinta na mallakan makamashin nukliya ta zaman lafiya ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments