Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa akwai bukatar kasashen Indiya da Pakisatan su daure su daina musayar wuta a tsakaninsu saboda tabbatar da zaman lafiya a yankin Asiya.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a safiyar yau Alhamis bayan isarsa birnin News Delhi.
A jiya larabace sojojin kasar Indiya suka cilla makamai masu linzami kan kasar Pakisatan da kuma yankin Kashamir da ke karkashinn ikon Pakisatn. Inda mutane 31n sauka rasa rayukansu a yayinda wasu 46 suka suka ji Rauni.
Shehbaz Sharif firai ministan kasarPakisatan ya bayyana cewa kasar Pakisatan zata rama, kuma ya sha alwashin maida martani kan duk wani jinin mutanen Pakisatan da sojojin Indiya suka zubar.
Har’ila yau ministan harkokinn wajen kasar Iran ya je kasar ta Indiya ne don halattan taron kwamitin tattalin arziki na hadin giwa tsakanin kasashen biyu. Ministan ya kara da cewa zai tattauna da tokwaransa na kasar Indiya kan yakin da ya barke a tsakanin kasashen biyu.
Sannan a wani labarin kuma kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Bakaei ya bayyana cewa kasashen Indiya da Iran zasu rattaba hannu a kan wasu yarjeniyoyi tsakanin kasashen biyu a wannan ziyarar Aragchi zuwa kasar ta Indiya.