Aragchi: An Cimma Wani Matsayi Wanda Su Ne Asasin Tattaunawa Tsakanin Iran Da Amurka

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa a tattaunawar jiya Talata dangane da shirin kasar na makamashin Nukliya a birnin Jeneva tsakanin

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa a tattaunawar jiya Talata dangane da shirin kasar na makamashin Nukliya a birnin Jeneva tsakanin Iran da Amurka an kai wani matsayi wanda shi ne asasin tattaunawar, kuma bangarorin biyu sun amince da wannan ci gaban da aka samu.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Aragchi yana fadar haka a taron bayan labarai da ya kira bayan taron bangarorin biyu a Geneva, wanda ya bayyana shi a matsayin ci gaba.

Y ace kafin haka ya gana da babban sakataren hukumar makamashin Nukliya IAEA Rafael Grossy inda suka yi magana kan ra’ayoyi daban daban wadanda suka tattauna a kansu a babban taron na Geneva.

Ya ce, a tattaunawar na jiya dai muna iya cewa an kai matsayin da ana iya fara rubuta wasu al-amuran da aka cimma matsaya a kansu dangane da shirin makamashin Nukliya a kansu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted