Jami’an tsaron kasar Iran sun ja kunnen Amurka da HKI kan sake fadawa kasar da Yaki, sun ce a wannan karon martani kasar sai ya fi na da tsanani.
Manjo Janar Mohsen Rezaei sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya bayyana a jiya Talata a kuma shafinsa na X, kan cewa babu wata tattaunawa da Amurka sai ta fara daukan mataki na farko don gina aminci tsakanin bangarorin biyu.
Kuma hakan zai faru ne kawai da cika sharuddan da JMI ta shimfida na yin hakan.
Hakama shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Bakir Qalibof, ya bayyana cewa tsagaita budewa juna wuta na din din din da Amurka zai faru ne kawai idan washington ta cika sharuddan Tehran guda 7.
Qalibof yana kara da cewa “Amurka ce ta fara farwa kasar da yaki, kuma ita ce ta fara wannan kuskuren wanda ya jefata cikin matsalolin da ta fada ciki, don haka ita ce zata fara daukar matakan da suka dace don gyara”. shugaban tawagar tattaunawa ta Iran ya bayyana haka ne a lokacinda yake tattaunawa da babban hafsan sojojin kasar Pakistan Field Marshal Asim Munir a nan Tehran a jiya Talata.