Kungiyar gwagwarmaya ta Ansarullah ta bayyana cewa yarjejeniyar tsagaiat wutar da ta cimma da Amurka, ba ta sauya matsayin kasar ba na kai wa Isra’ila hari.
Kakakin kungiyar Ansarullah Mohammed Abdul-Salam ya jaddada cewa Dakarun Yeman za su ci gaba da kai hare-hare kan Isra’ila domin goyan bayan Falasdinawa a zirin Gaza.
Yarjejeniyar da Amurka ba ta da alaka da matsayinmu na goyan bayan Gaza, inji Abdul-Salam.
A jiya ne masarautar Oman ta sanar cewa Amurka da kungiyar Ansarullah da aka fi sani da ta ‘yan Houtshis a Yeman suka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Oman ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa: Bayan tattaunawa da tuntubar juna da aka yi a baya-bayan nan da kuma tuntubar juna tsakanin masarautar Oman ta Amurka da hukumomin da abin ya shafa a birnin Sana’a na jamhuriyar Yeman, an samu cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu.
Sanarwar ta kara da cewa: A nan gaba, ko wanne bangare ba zai kai hari kan daya ba, ciki har da jiragen ruwan Amurka a tekun Bahar Rum da Bab al-Mandab, domin tabbatar da ‘yancin zirga-zirgar jiragen ruwa da kuma tafiyar da harkokin kasuwancin kasa da kasa cikin sauki.