Search
Close this search box.

An Yi Ganawa Tsakanin Wasu Jiga-jigan Kungiyoyin Gwagwarmayar Falasdinawa

Wasu manyan jami’ai daga kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa na Hamas da Islamic Jihad da ke Zirin Gaza sun gana a Doha babban birnin kasar Qatar, inda

Wasu manyan jami’ai daga kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa na Hamas da Islamic Jihad da ke Zirin Gaza sun gana a Doha babban birnin kasar Qatar, inda suka tattauna batutuwan siyasa da lamura na baya-bayan nan dangane da yakin da gwamnatin Isra’ila ke ci gaba da yi na kisan kare dangi a kan gabar tekun.

Taron ya gudana ne a hedkwatar kungiyar Hamas da ke birnin Doha a ranar Larabar tsakanin wata tawaga da ta fito daga shugabancin kungiyar da Ziyad al-Nakhala, babban sakataren kungiyar Jihad Islami, da mataimakinsa Mohammad al-Hindi.

“Sun jaddada wajabcin dakatar da wuce gona da iri da ake yi wa Falasdinawa da kuma dorawa jami’an mamayar alhakin laifukan da suka aikata na cin zarafin bil’adama,” in ji Hamas a cikin wata sanarwa.

Tun a watan Oktoban shekarar da ta gabata ne gwamnatin Isra’ila ta kaddamar da yakin Gaza a matsayin martani ga wani harin ba zata na Hamas.

Akalla Falasdinawa 40,223 akasari mata da kananan yara ne aka kashe yayin da wasu 92,981 suka jikkata.

Duk wani yunskuri na cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ya cutura kawo yanzu, duk da cewar Amurka ana bukatar cimma yarjeejniyar data danganda da dama.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments