Shugaban kungiyar ‘al-Hikimah” na kasar Iraki Ammar Hakim ya gana da shugaban kasar Masar Abdulfattah al-sisi. A yayin ganawar Ammar Hakim ya jaddada muhimmancin taimaka wa kokarin da Masar take yi na ganin an hana korar falasdinawa daga yankunansu zuwa wajen Falasdinu.
Ammar Hakim ya kuma ce, a yayin wannan ganawar na bayyana wa shugaban kasar jinjinawarmu akan yadda Masar ta kasance mai taimaka wa Falasdinawa.”
Haka nan kuma mun nuna goyon bayanmu ga kokarin Masar al’umma da gwamnati na hana tilasatawa Falasdinawa yin hijira da kuma kare hakkokin Falasdinawa da riko da kasarsu.
Har ila yau Ammar Hakim ya ce ganawar tasu ta tabo batutuwa da su ka shafi halin da ake ciki a wannan yankin da kuma wajabcin aiki a tsagaita wutar yaki a yankin Gaza.
Sayyid Ammar Hakim ya kuma yi ishara da muhimmanci sake gina yankin na Gaza ba tare da an fitar da mazaunansa daga ciki ba. Bugu da kari bangarorin biyu sun jaddada muhimmanci kafawa Falasdinawa daularsu akan iyakokin 1967 da birnin Kudus zai zama babban birninta domin haka ne hanyar samar da zaman lafiya a cikin wannan yankin.
Akan halin da ake ciki a matakin wannan yankin kuwa, Sayyid Ammar Hakim ya ce; Kasar Iraki tana son ganin an sami zaman lafiya a cikin wannan yankin da kuma warware sabanin da ake ciki a wannan yankin da kusanto da fahimtar juna a tsanakin bangarori mabanbanta.