An samu bullar sabani da rikici a tsakanin ‘yan sahaypniyya game da mamaye Gaza a daidai lokacin da ake ci gaba da kai hare-hare da kuma rage yawan sojojinsu a yankin
Yakin kisan kiyashi yana ci gaba da gudana a Gaza ta hanyar ci gaba da kai hare-hare kan mai uwa da wabi, tare da nau’o’i daban-daban na aiwatar da kashe-kashe da kuma kakaba yunwa. Duk da yadda kasashen duniya ke ci gaba da nuna bacin ransu kan irin girman kai da gwamnatin mamayar Isra’ila ke nuna wa, kafafen yada labaran haramtacciyar kasar isra’ila sun rawaito cewa: Majiyar fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu ta bayyana cewa ya yanke shawarar mamaye yankin gaba daya da aka killace saboda yana son warware yakin da ake yi da kungiyar Hamas.
Majiyar ta kara da cewa: Idan matakin mamaye yankin gaba daya bai dace ba, to shugaban rukunin sojojin mamayar Isra’ila Eyal Zamir za iyi murabus. A cikin wannan yanayi, ministan tsaron cikin gida Itamar Ben-Gvir ya bayyana cewa, dole ne babban hafsan hafsoshin rundunar sojin Isra’ila ya fayyace a fili cewa, yana cikakken bin umarnin bangaren siyasa, ko da kuwa an yanke shawarar mamaye zirin Gaza.