An Sake Zaben Qalibof A Matsayin Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Iran

Majalisar dokokin kasar Iran ta sake zaben Mohammad Baqir Qalibof a matsayin shugaban majalisar dokokin kasar na wata shekara a zaben da aka gudanar a

Majalisar dokokin kasar Iran ta sake zaben Mohammad Baqir Qalibof a matsayin shugaban majalisar dokokin kasar na wata shekara a zaben da aka gudanar a cikin majalisar a jiya Litinin.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran,  ya bayyana cewa ya sami kuriu 219 daga cikin Jimillan kuri’u 272, wanda ya bashi babban rnjaye a kan sauran wadanda suke takara da shi. Wannan kuma ya nuna cewa shugaban majalisar ya na da karbuwa a cikinta. Kuma yana da tasiri a cikin al-amuran gwamnati musamman a lokacinda kasar take fama da barazana a ciki da wajen kasar, musamman dangane da tattaunawa kan shirin makamashin Nukliyar kasar, wanda ake tattaunawa a kansa da Amurka.

An gudanar da wasu zabubbuka a cikin majalisar tare da fitar da yan majalisun da suka dace wajen rike su.

Akan gudanar da zabe don rike wasu mukamai a majalisar dokokin kasar Iran ne a ko wace shekara. Yan majalisa da dama sun bayyana gamsuwarsu da shugaban Qalibof na shekarar da ta gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments