An Nada Mataimakin Babban Kwamandan Rundunar Yansanda Na Kasar Iran

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Ayatullahi Sayyid Aliyul Khaminae ya nada Eskandar Mumini, ministan harkokin cikin gida na kasar a matsayin

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Ayatullahi Sayyid Aliyul Khaminae ya nada Eskandar Mumini, ministan harkokin cikin gida na kasar a matsayin mataimakon babban kwamandan rundunar yansandan kasar Iran gaba daya.

Kamfanin dillancin labaran IRIB-NEWS ya nakalto ofishin jagoran juyin juya halin musulunci kuma babban kwamandan jami’an tsaron kasar Iran yana fadar haka a yau laraba, ya kuma kara da cewa daga ranar 24 ga watan Augusta na wannan shekarar Mumini ne zai rike mukamin mataimakin babban kwamandan rundunar yansandan kasar.

A wani Labarin kuma shugaban kasar Iran Masoud Pezeskiyan ya gabatar da Fatimah Muhajironi a matsayin sabon kakakin gwamnatin kasar, kuma ita ce ta mayi gurbin Ali Bahadari Jahrumi wanda ya kasance kakakin gwamnatin a gwamnatin marigayi shugaban Ra’isi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments