Kungiyoyin Falasdinawa mabanbanta ne su ka yi kira ga al’ummun duniya da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin raya ranar Kudus ta duniya.
Sanarwar da kungiyoyin na Falasdinu su ka fitar ta kunshi yin kira ne ga al’ummun musulmi da larabawa da kuma duk masu son ‘yanci a duniya da su fito a yau saboda su nuna fushinsu akan abinda yake faruwa a Gaza.
A can kasar Lebanon ma dai babban magatakardar kungiyar gwgawarmaya ta Hibzullah sayyid Hassan Nasrallah ya yi irin wannan kiran ga ganin mutane sun fito saboda nuna bacin ransu akan abinda yake faruwa a Gaza na kisan kiyashin da ‘yan sahayoniya suke yi wa Falasdinawa da barnata dukiyarsu da lalata rayuwa a yankin.
Wanda ya assasa juyin juya halin musulunci na Iran ne marigayi Imam Khumaini ( r.a) ya ayyana juma’ar karshe ta kowance azumin watan Ramadana a matsayin ranar Kudus ta duniya domin fadakarwa akan halin da Falasdinu da kuma masallacin Kudus suke ciki a karkashin mamayar HKI.
Daga kasar Yemen ma jagoran kungiyar Ansarullah Sayyid Abdulmalik al-Husi ya yi ya bayyana ranar Kudus ta bana a matsayin wacce za a gabatar da ita a cikin yanayi na musamman saboda yakin da HKI take yi da al’ummarFalasdinu.