An Kashe Wani Babban Jami’in Kungiyar Hizbuiiah Na Kasar Lebanon A Yankin Yammacin Bikaa

Wata majiyar tsaro ta kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta bada labarin cewa wani dan bindiga ya harbe wani babban jami’ii kuma malaman addini na

Wata majiyar tsaro ta kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta bada labarin cewa wani dan bindiga ya harbe wani babban jami’ii kuma malaman addini na kungiyar Hizbullah a yammacin yankin Biqaa.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya nakalto majiyar tana cewa, wani dan bindiga wanda ba’a ganeshi shi har yanzun, ya harbe Shiekh Mohammad Hammadi a yankin na Biqaa a lokacinda yake tsaya a kofar gidansa a garin Machghara a jiya Talata.

Labarin ya kara da cewa an kai Hammadi zuwa bayan da wasu a cikin motoci biyu suka harbeshi, amma ya rasu daga baya a asbiti.

Jami’an yansanda a yankin sun killace garin suna kuma gidanar da bincike don gano wadanda suke kashe Shiekh Hammadi. Sai dai haryanzun basu bada wani labara dangane da kissan ba.  Yankin Biqaa dai yana kusa da kan iyaka da kasar Siriya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments