Bayanai daga Falasdinu na cewa an kashe Muhammed Jabber daya daga cikin manyan mayakan Falasdinawa a yankunan Yamma da Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye.
Ƙungiyar Palastenian Islamic Jihad ta ce Jabber ya yi shahada, inda kuma ta yi alkawarin daukar fansar kisan nasa.
Abu Shujaa kamar yadda aka fi sanin sa, an haife shi a sansanin yan gudun hijra na Nur Shams kuma shi ne kwamandan mayakan da ke Tulkram wani tsagi na kungiyar mayakan Faladinawa ta Palastenian Islamic Jihad.
A watan Afrilu sojojin Isra’ila sun ayyana neman sa, inda kuma bayan kwanaki biyu sai aka gan shi a wata jana’izar wani dan gwagwarmaya.
Dakarun Isra’ila sun ce an kashe Jabber ne tare da wasu mutum hudu a cikin wani masallaci da suka buya.
Dakarun sun zargi Jabber da kitsa harbe wani farar hula mai suna Amnon Muchtar a watan Yuni.