An kamala gudanar da zabe a yankin jabal Lebanon na kasar Lebanon a safiyar yau Lahadi har an kuma an fara irge.
Tashar talabijin ta Almanar ta kasar ta bayyana cewa an bude rumfunan zabe tun karfe 7 na safe, kuma an kamala zaben da yamma.
Sannan ma’aikatar cikin gida da kuma kananan hukumomi ta bayyana cewa mutanen da suka fito don kana kuri’insu ya kai kimani kashi 45.% da yan kai.
Yankin Jabal Lobnon dais hi ne yanki mafi yawan mutane a kasar kuma yanki ne wanda hizbullah take da masu goyon baya da dama.
Matsalolin daya dayan daya, wadanda suka hada da rashin kudade da rashin gwamnati ya hana a gudanar da zabubbuka kananan hukumomin wanda yakamata a gudanar tun shekara ta 2016.
Har’ila yau yakin tsakanin kungiyar Hizbullah da kuma HKI suna daga cikin al-amura da suka kawo jinkirin zaben.