An Kafa Kwamitin Duba Dukkanin Madatsun Ruwa Da Ke Cikin Tarayyar Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta kafa wani kwamiti da zai yi nazarin halin da dukkanin madatsun ruwan Nijeriya ke ciki bayan ambaliyar ruwan da ta auku a

Gwamnatin Tarayya ta kafa wani kwamiti da zai yi nazarin halin da dukkanin madatsun ruwan Nijeriya ke ciki bayan ambaliyar ruwan da ta auku a Jihar Borno.

Wannan dai na daga cikin kudurorin da aka cimma a taron majalisar zartarwa da Shugaban Tinubu ya jagoranta a ranar Litinin.

Ministan yada labarai, Mohammed Idris ne, ya shaida wa manema labarai cewar, a kowane lokaci idan abu ya faru mara dadi ko kuma wanda za a dauki darasi a kansa, to gwamnati kan sake lamarin don kaucewa faruwar hakan a gaba.

Ya ce, “Ba daidai ba ne idan an samu makamancin abin da ya faru a Maiduguri a yi shiru kamar babu abin da ya faru, hakan ne ya sa majalisar zartaswa ta yi tunanin cewa ba kawai maganar madatsar ruwa ta Alau ba, akwai bukatar a sake duba duk wata madatsar ruwa da ke Nijeriya.

“Kwamitin da aka kafa yanzu zai sake duba dukkanin madatsun ruwa don tabbatar da cewa ba a sake samun aukuwar irin abin da ya faru a Maiduguri ba.”

dris, ya ce a yanzu gwamnati ta yi duk abin da ya kamata dangane da batun cikakken bayani a kan wannan kwamiti.

Ambaliyar dai ita ce mafi muni a Jihar Borno cikin shekaru 30, saboda ta shafe sassan Maiduguri da dama, Lamarin dai ya haifar da asarar rayuka da dukiyoyi marasa adadi a jihar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments