An Gudanar Da Makokin Tasu’a Na Imam Hussain (s) A Husainiyyar Imam Khomanini(q) Tare Da Jagora

An gudanar da makokin daren tasu’an Imam Hussain (a) a wurare da dama a ciki da wajen kasar Iran. Daga ciki har da hussainiyyar Imam

An gudanar da makokin daren tasu’an Imam Hussain (a) a wurare da dama a ciki da wajen kasar Iran. Daga ciki har da hussainiyyar Imam Khomaini (q) wanda yake gidan jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Ayatullahi Sayyid Aliyul Khamanae.

Ofishin jagoran juyin juya halin musulunci ya bayyan cewa Hujjatul Islam wal-muslimina Ma’ud Aali ne ya gabatar da jawabi dangane daren Tasu’a da kuma irin halin da Imam Hussain (s) jikan manzon All..(s) suke kasance a daren na 9 ga watan Muharram a hamadar Karbala. Musamman rashin ruwan sha da suke fama da shi saboda toshe hanyar ruwan kogin Furat wanda sojojin Yazid ko Dan Marjana suka yi.

Har’ila yau a taron na Tasu’a , Sannan mas’ud karimi ya karanta makokin daren tasu’a. Inda a ciki ya ambaci irin jaruntar da Abufadlil Abbas ya nuna a kokarin samarwa yaran Imam Hussain(a).

Miliyoyin mutane a cikin Iran a wasu kasashen duniya sun raya wannan daren mai al-barka don tunawa da shahidan Karbala.

Yau litinin ce 9 ga watan muharram shekara ta 1446 bayan hijira, wato ranar tasu’an Imam Hussain na wannan shekarar. Shekari 1,385da suka gabata wato tasu’an shekara ta 61 bayan hijira.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments