An gudanar da makokin daren tasu’an Imam Hussain (a) a wurare da dama a ciki da wajen kasar Iran. Daga ciki har da hussainiyyar Imam Khomaini (q) wanda yake gidan jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Ayatullahi Sayyid Aliyul Khamanae.
Ofishin jagoran juyin juya halin musulunci ya bayyan cewa Hujjatul Islam wal-muslimina Ma’ud Aali ne ya gabatar da jawabi dangane daren Tasu’a da kuma irin halin da Imam Hussain (s) jikan manzon All..(s) suke kasance a daren na 9 ga watan Muharram a hamadar Karbala. Musamman rashin ruwan sha da suke fama da shi saboda toshe hanyar ruwan kogin Furat wanda sojojin Yazid ko Dan Marjana suka yi.
Har’ila yau a taron na Tasu’a , Sannan mas’ud karimi ya karanta makokin daren tasu’a. Inda a ciki ya ambaci irin jaruntar da Abufadlil Abbas ya nuna a kokarin samarwa yaran Imam Hussain(a).
Miliyoyin mutane a cikin Iran a wasu kasashen duniya sun raya wannan daren mai al-barka don tunawa da shahidan Karbala.
Yau litinin ce 9 ga watan muharram shekara ta 1446 bayan hijira, wato ranar tasu’an Imam Hussain na wannan shekarar. Shekari 1,385da suka gabata wato tasu’an shekara ta 61 bayan hijira.