Miliyoyin mutanen kasar Iran sun gudanar da jana’izar shahidai kimani 300, a duk fadin kasar, a dai-dai lokacinda ake makokin shahadar diyar manzon Allah (s) Fatimah Azzahra (s).
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, shahidan, wadanda har yanzun ba’a tantance su ba, an ganosu a wurare daban-daban a cikin kasar Iraki inda suka yi shahada a yakin shekaru 8 tsakanin Iran da Iraki a farko-farkon nasarar juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran, tsakanin shekara (1980-1988).
Ya zuwa yanzu dai an gano gawakin shahidai fiye da 45,000, tun bayan kawo karshen yakin sannan akwai wasu fiye da 2000 wadanda ake neman inda suke a cikin kasar ta Iraki.
Labarin ya kara da cewa a nan Tehran kadai an yi jana’izar shahidai 100. Sannan sauran gawakin shahidan, wadanda aka ganosu a tsibirin Maimoon da Shalamce, an yi masu jana’iza a lardin Golestan, Qom, Fars, Sistan da Baluchestan, Ardabil, gabacin Azerbaijan da wasu wurare.
Wadannan shahidan sun yi shahada ne a ayyukan farmaki na Kheibar, Karbala-4, Karbala-5, da kuma Valfajr-1.