Bayan nasarar da gamayyar jam’iyyun hannun dama da kuma Social Democrats a zaben majalisar dokokin kasar zagaye na biyu a kasar Faransa, an fara tashe tashen hankula a garuruwa da dama a kasar.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kafafen yana labarai na kasar ta Faransa na cewa tashe tahen hankulan sun hada da birnin Paris babban birnin kasar.
Labarin ya kara da cewa, matasa masu goyon bayan jam’iyyu daban daban sun yi ta lalatakayakin jama’a da kuma fada da yansanda a wurare daban daban a birnin Paris.
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron wanda ya rage masa shekaru uku ya kamala wa’adin mulkinsa, da kuma kasancewa ba zai iya gudanar da wani zabe ba har zuwa shekara guda mai zuwa, a halin yanzu dole ne ya nemi wasu hanyoyi da kula da majalisar dokokin kasar wacce take ciki da rikici, rikicin da yake iya shafar harkokin cikin gida da na wajen kasar.