An Fara Jana’izar Shahid Manjo  Janar  Abbas Nilofurshan Anan Birnin Tehran

Da misalin karfe 8: 30 na safiyar yau a nan birnin Tehran aka fara bankwana da shahid manjo janar Abbas Nilofurushan wanda ya yi shahada

Da misalin karfe 8: 30 na safiyar yau a nan birnin Tehran aka fara bankwana da shahid manjo janar Abbas Nilofurushan wanda ya yi shahada tare da Sayyid Hassan Nasrallah a birnin Beirut.

Daga cikin wadanda su ka halarci wajen da ake ban kwana a shahidin da akwai kwamandan rundunar kudus dake karkashin dakarun kare juyin juya halin musulunci ta Iran ( IRGC), Janar Isma’ila Aqa’ni, sai kuma kwamandan rundunar kare juyin musulunci janar Husain Salami.  Haka nan kuma Babban mai shigar da kara na kasa Muhammad Ja’afar Muntazari, haka nan kuma kwamanan sojan kasa na rundunar kasa ta Muhammadu Rasulullah (s.a.w), janar Hasan Hassan.

Dubun dubatar mutane ne suke halartar taron wanda har yanzu haka yana cigaba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments