A cika tsawon kwanaki 222 da fara aiwatar da yaki kisan kare dangi kan al’ummar Falasdinu a Zirin Gaza
Yakin da sojojin mamayar gwamnatin yahudawan sahayoniyya suke yi a Zirin Gaza ya shiga rana ta 222, a daidai lokacin da sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya suke ci gaba da yin ruwan bama-bamai a yankuna da dama a yankin Gaza, wanda hakan yake sanadiyyar shahada da jikkatan Falasdina musamman mata da kananan yara.
A halin da ake ciki kuma, gwagwarmayar Falasdinawa ta koyar da ‘yan mamayar yahudawan sahayoniyya wani sabon darasi mai tsauri bayan da ta janyo wa rundunar sojin mamaya dimbin hasara na rayuka da tarwatsa motocinsu na yaki.