An gudanar da bikin cika shekaru 41 da kafa kungiyar hadin guiwa ta tatalin arziki ta ECO a nan birnin Tehran ne a jiya litinin inda sakatare janar din kungiyar Eco Majeed khan da ministan aladu reza salihi –amiri suka gabatar da jawabai a wajen, da ya shafi irin ci gaba da kungiyar ta samu a cikin wadannan shekaru da kuma bayyana muhimmancin yin aiki tare .
Kungiyar Eco tana daga cikin mihimmiyar hanya ta duniya da ta fara daga yankin tekun fasha zuwa tsakiyar asiya , kuma kasashen dake mambobin kungiyar sun kai kusan rabin biliyan dake da arzikin makamashi da ma’adinai kasa, baya ga batun tattalin arziki , kungiyar tana matsayin jigo mai muhimmanci wajen huldodin diplomasiya a yankin. Musamman ma ga kasar iran,da take bada dama ga mambobinta yin huldar kasuwanci, zirga-zirga da kuma abubuwan da suka shafi al’adu.
Kungiyar da iran ta kirkiro tare da turkiya da Pakistan kafin daga baya aka fadadata zuwa mambobi guda 10 wato Iran, turkiya, Pakistan ,Azarbaijan ,Afghanistan , turkuminstan, Uzbakestan da kyargistan da kuma kasar Tajikistan, kasashen suna fatan kara ingantan kasuwanci dake tsakaninsu, da kuma kafa hanyoyin sadarwa , da hadin guiwa a bangaren makamashi da wutar lantarki da shinfida bututu da kuma karfafa bangaren aladu da yawon bude ido.