A Amurka yau da dare ne ‘yan takara a zaben shugaban kasar mai zasu fafata a muhawarar talabijin mai muhimmanci a siyasar kasar.
Za a yi muhawarar tsakanin Donald Trump da Kamala Harris wadda ita ce karo na farko da ‘yan takarar biyu za su fafata.
Mintuna 90 na muhawarar zasu zama zakaran gwajin dafi ga ‘yan takaran.
Rashin tabuka abin kirki da shugaba Joe Biden ya yi a muhawarar ta farko a karshen watan Yuni, ya janyo matsin lamba a cikin jam’iyyarsa ta Democrat har ta kai shi ga janye aniyarsa ta sake tsayawa takarar shugaban kasar.
Kuri’ar jin ra’ayin jama’a da jaridar New York Times ta yi, ta nuna cewa
zaben zai kasance mai zafi.